Professor Ahmad Hausa Novel Part 1

                    Professor Ahmad







                   Ibrahim Auwal

                                   
                                      1
Game da Marubuci
Suna na Ibrahim Auwal dalibi ne ni a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
Game da Littafi
Wannan littafi ne na adabi da al’adar hausawa wanda yake kunshe da darussan rayuwa kala kala.
Na rubuta littafin a shekarar dubu biyu da goma sha hudu (2014).
Na fara  buga littafin a matsayin pdf a shekarar dubu biyu da sha tara (2019).
Hakkin Mallaka
Ba yarda wani/wata ya/ta yi anfani da wani bangare ko sashe na wannan littafi ba sai da izinin mawallafi.
©Ibrahim Auwal
Waya:- +2348060082079
Adreshin yanar gizo:-hausanovels.net@gmail.com
hausanovels.net





                           2
                Farfesan Kimiyya
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, mai kowa mai komai, mai yanda yaso alokacin da yaso, akan wanda yaso, ko anaso ko ba a so.
Acikin garin kano akwai wata anguwa da kiranta Wudil, ya kasance a wannan babban gari akwai wata babbar jami’ar kimiyya da fasaha, wadda acikin akwai kwararrun malamai wadanda suke da zunzurutun ilimin kimyya da fasaha, amma malamin da yafi suna kuma yafi kwarewa a wannan fage a jami’ar sunansa farfesa Ahmad, hakan ya faru ne sanadiyyar ilimin da yake dashi na Alqur’ani mai girma domin yasansa da kuma kimiyyarsa zuryan.
Farfesa irin mutanenannanne wadan basu da yawa acikin jama’a, bai taba cut aba tun farkon rayuwarsa, shi mutumne mai gaskiya acikin al’ummarsa, sanadiyyar gaskiyar da addu’o’I ya samu shahara acikin fadin garin kano.
Wata rana farfesa Ahmad yan koyar da dalibansa ilimin kimiyyar rayuwa wanda a harshen turanci ake kira biology, sai wani daga cikin daliban ya masa tambaya yana mai cewa “mallam wai taya ne aka samo asalin halittar mutuum?”
Sai farfesa Ahmad yace “kayi tambaya mai anfani, amsar da zan iya baka shine:”
Duk mutanen duniya sun yarda cewa Allah sine maqagin kowa da komai, said ai wasu yan tsurarun addinai da suke bin rayuwa da ka bada hujja basai tunanin “wajadna aba’ana” wato “munga iyayenmu sunayi”,
                                                            3
misalign wadannan addini shine addini darwiniyanci.

         

Post a Comment

0 Comments